Wasanni

Fabregas zai koma Chealsea

Dan wasan Spain Cesc Fabregas
Dan wasan Spain Cesc Fabregas REUTERS/Juan Medina

Kungiyar Barcelona dake wasa a gasar La ligan kasar spain ta bayar da sanarwar sayar wa Chelasea ta Ingila, dan wasanta na tsakiya mai suna Cesc Fabregas. Rahotanni na cewa Fabregas mai shekaru 27 a duniya, da ke cikin tawaggar ‘yan wasan kasar Spain, da zasu yi wasa a gasar cin kofin duniya a Brazil, ya sa hannu ne kan kwantaragin shekaru 5, kan kudaden da suka kai Fam din ingila miliyon 30, kwatankwacin Dalar Amurka Miliyon 50 da rabin Miliyon.