Brazil 2014

Neymar ya ja tawaga a Twitter

Neymar  tauraron Brazil a gasar cin kofin duniya a bana.
Neymar tauraron Brazil a gasar cin kofin duniya a bana. REUTERS/Damir Sagolj

Neymar na Brazil ya ja tawagar mabiya a shafin Twitter, inda masoya kwallon kafa daga kasashe sama da 150 suka aiko da sakwanni miliyan goma sha biyu, da dubu dari biyu bayan Brazil ta doke Croatia ci 3 da 1, Kuma Neymar shi ne Dan wasan da aka fi ambata a cikin sakwannin na dimbin mutanen duniya a Twitter.

Talla

Kamfanin Twitter yace shafin ya smau dimbin mabiya bayan bude wasannin gasar cin kofin duniya a Brazil.

Tun da farko ne, masu kula da mabiya shafin Twitter suka yi hasashen cewa za’a samu dimbin mutane da zasu yi mu’amula da shafin a gasar cin kofin duniya fiye da wani al’amari day a hada kasashen duniya a waje daya.

Gasar Cin Kofin Duniya a Brazil

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.