Brazil 2014

Za mu buge Spain-Van Gaal

Louis van Gaal, Kocin Netherlands
Louis van Gaal, Kocin Netherlands eurosport.com

Sabon kocin Manchester United da ke jagorantar Netherlands a gasar cin kofin duniya a Brazil yace duk da sun san girman Spain a fagen taka leda amma zasu gane shayi ruwa ne domin zasu dauki fansan dukan da suka sha ne a gasar da aka gudanar a Afrika ta kudu.

Talla

Idan an jima ne za’a yi karabkiya tsakanin Spain da Netherlands, inda za’a maimaita karawar karshe da kasashen suka yi a gasar cin kofin duniya da aka gudanar a Afrika ta kudu.

Spain ce ta lashe kofin gasar shekaru hudu da suka gabata bayan ta doke Netherlands a wasan karshe, amma Van Gaal yace yana da yakinin haduwarsu a Brazil zasu ba Spain mamaki.

Kocin yace zasu kare gidansu tare da kai wa Spain hare hare domin ita ce hanyar da zasu doke Spain.

Amma kocin Spain Del Bosque yace Spain ba ta shakkun kowa a Brazil saboda tarin zaratan ‘Yan wasan shi.

An dai hada Spain ne da Netherlands a rukunin B tare da Chile da Australia, wadanda dukkaninsu zasu kece raini a yau Juma’a.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.