Brazil 2014

Cote d’Ivoire ta doke Japan

'Yan wasan Cote d'Ivoire Gervinho da Didier Drogba a Brazil
'Yan wasan Cote d'Ivoire Gervinho da Didier Drogba a Brazil REUTERS/Ruben Sprich

Kasar Cote d’Ivoire ta zirara kwallaye biyu a ragar Japan cikin minti biyu wanda ya ba kasar daga Nahiyar Afrika nasarar lashe wasan da aka tashi ci 2 da 1 a zagayen farko na gasar cin kofin duniya da ake gudanarwa a Brazil. Japan ce ta fara jefa kwallo a ragar Cote’Ivoire ana minti 16 da fara wasa.

Talla

Amma cikin mintina biyu Cote d’Ivoire ta jefa kwallaye biyu ana mintina 64 da 66 bayan dawo wa hutun rabin lokaci kuma Wilfried Bony da Gervinho ne suka zirara kwallayen a ragar Japan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.