Brazil 2014

Karuwai sun taka leda a Brazil

Karuwai suna taka kwallo a Brazil lokacin da ake gudanar da gasar cin kofin Duniya.
Karuwai suna taka kwallo a Brazil lokacin da ake gudanar da gasar cin kofin Duniya. AFP

Karuwai a kasar Brazil sun gudanar da wasan kwallon kafa inda suka kara da wata kungiyar Mata Kiristoci mabiya darikar Evangelic a Belo Horizonte, domin yada fatawar ‘Yancin mata masu sana’ar karuwanci a duniya. Karuwan sun fafata ne bayan kammala wasa tsakanin Colombia da Girka a gasar cin kofin Duniya da ake ci gaba da gudanarwa a Brazil.

Talla

Karuwan sun kara ne da tawagar Kungiyar Mata Kiristoci da zuka shigo Brazil daga Amurka kuma sun sanya rigar kwallo mai yanayi da tutar Brazil.

Matan sun ce sun gudanar da wasan ne domin nuna wa duniya suna da ‘yanci.

An dade Karuwai a Brazil suna kira ga gwamnatin kasar ta kula da su kamar yadda ake kula da dukkanin fanoni a kasar.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.