Kwallon kafa

Okocha ya koka da gazawar Keshi a wasan Najeriya da Iran

Tsohon dan wasan Najeriya, Austin Jay Jay Okocha
Tsohon dan wasan Najeriya, Austin Jay Jay Okocha www.google.com

Tsohon dan wasan Najeriyar Jay Jay Okocha ya nuna alhininsa kan yadda Najeriya ta yi kasa a gwiwa a wasanta da Iran a gasar cin kofin wasan kwallon kafa na duniya, inda ya ce wannan dama da Najeriya ta zubar, kamata ya yi a ce ta samu nasara.

Talla

Hasali ma Okocha ya dora laifin wannan rashin nasara akan mai horar da ‘yan wasan Stephen Keshi, inda ya kara da cewa bai dauki lokaci wajen horas da ‘yan wasan a fannin basirar buga wasa ba.

Okocha ya kuma soki Keshi  kan yadda ya canja dan wasansa Victor Moses a zagaye na biyu inda ya sako shola Ameoba.

Najeriya za ta kara da kasar Bosnia ne a wasanta na gaba, wasan da zai zamanto dole Najeriyar ta lashe muddin ta na so ta tabuka wani abu a gasar.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.