Kwallon kafa

Brazil da Mexico sun tashi canjaras, Belgium ta doke Algeria

Mai tsaron ragar Mexico, Guillermo Ochoa
Mai tsaron ragar Mexico, Guillermo Ochoa www.goal.com

Kasar Brazil mai daukan bakuncin gasar cin kofin duniya na wasan kwallon kafa, ta tashi canjaras da kasar Mexico, bayan da bangarorin biyu suka fafata a filin wasa na Forteleza dake kasar ta Brazil a daren jiya.

Talla

Sai dai duk da cewa akwai fitattun ‘yan wasa a wannan karawa da aka yi, mai tsaron ragar Mexico, Guillermo Ochoa, shine ya fi haskawa a wannan wasa, saboda irin kwallaye da ya hana shiga cikin raga.

Tuni dai aka yi ta yaba bajintar da Ochoa ya nuna, inda shi kanshi mai horar da ‘yan wasan Brazil Luis Scolari ya jinjina mai.

An dai kwashe zagaye na farko da na biyu bangarorin biyu suna kai hare hare ga junansu, ba tare da sun kai ga gaci ba.

Ta wata fuska wannan karawa, ta kara tabbatar da tarihin da kasar Mexico ta kafa, na kasancewa babban kalubale ga Brazil a duk lokacin da suka hadu.

Ko a shekarun baya da suka hadu a wasan karshe na gasar Olympics, Mexico ta doke Brazil, ko da yake ta dauki fansa a gasar nahiyoyin duniya da Brazil din ta dauki bakunci a bara.

Kamin wannan wasa a rukunin H, an fafata kuma tsakanin Algeria da Belgium inda aka doke Algeria da ci 2-1.

Sofiane Feghouli ne dai ya fara zirawa Algerian kwallonta a raga a cikin minti na 25.

Daga baya Belgium ta farke kwallon a cikin minti na 70 ta kuma kara wata kwallo a cikin minti na 80.

A daya bangaren kuma Rasha da Koriya ta Kudu, sun tashi da ci 1-1. Koriya ce ta fara zira kwallon ta a cikin minti na 68, inda daga baya kuma Rasha ta farke kwallon a cikin mintina shida.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.