Kwallon kafa

Shin Spain za ta kai labari a hanun Chile?

'Yan wasan kasar Spain
'Yan wasan kasar Spain fifa.com

A wasannin da za a buga a yau Laraba a ci gaba da karawa a gasar cin kofin duniya na kwallon kafa, kasar Spain za ta kara ne da kasar Chile.

Talla

Daya na kallon wannan wasa a matsayin wanda zai fi daukan hankulan masoya kwallon kafa, ganin yadda Spain din ta kaya a wasanta na farko.

Chile dai ta yi nasarar wasanta na farko da Australia da ci 3-1 yayin da Netherland ta doke Spain din da ci 5-1 a wasanninsu na farko.

Muddin kuma Chile ta doke Spain a wannan rukuni na B, sannan Netherland ta kaucewa faduwa a wasanta da Australia, Spain wacce ke rike da kofin, za ta fice daga wannan gasa.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.