Brazil 2014

Kamaru ta sha kashi

'Yan wasan Kamaru Benjamin Moukandjo da Benoit Assou- Ekotto suna fada da juna
'Yan wasan Kamaru Benjamin Moukandjo da Benoit Assou- Ekotto suna fada da juna REUTERS/Murad Sezer

Kasar Kamaru ta kasance kasa ta farko daga Nahiyar Afrika da aka yi waje da ita a gasar cin kofin duniya da ake gudanarwa a Brazil, bayan ta sha kashi ci 4 da 0 a hannun Croatia. Yanzu Croatia tana da yakinin tsallakewa zuwa zagaye na biyu a gasar a rukuninsu na A idan har ta samu nasara a wasanta na gaba.

Talla

A karawar farko Croatia ta sha kashi ne a hannun Brazil, amma nasarar da kasar ta samu akan Kamaru tana iya tsallakewa zuwa zagaye na biyu.

Akwai Jan kati da alkalin wasa ya ba Dan wasan Kamaru Alexandre Song, tun kafin aje hutun rabin lokaci.

Akwai ‘yan wasan Kamaru guda biyu Benoit Assou-Ekotto da Benjamin Moukandjo da aka nuna suna fada da juna a lokacin da suke shan kashi a hannun Croatia.

Yanzu Croatia tana matsayi na uku ne a teburin rukuninsu na A, tazarar maki guda tsakaninta da Brazil da Mexico da ke jagorancin Tebuurin. Kamaru ce ta karshe babu maki bayan ta sha kashi a hannun Mexico a karawa ta farko.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.