Brazil 2014

'Yan kallon Kwallo sun balle katangar Filin Maracana

'Yan kasar Chile suna murnar doke Spain a gasar cin kofin duniya da ake gudanarwa a Brazil.
'Yan kasar Chile suna murnar doke Spain a gasar cin kofin duniya da ake gudanarwa a Brazil. REUTERS/Stringer/Brazil/Lucas Landau

‘Yan sanda a Brazil sun cafke mutane 85 yawancinsu mutanen kasar Chile da suka balle katangar filin wasan Maracana a birnin Rio wadanda ke kokarin shiga filin wasa ta bayan fage a lokacin da Spain ke fafatawa da Chile. Wannan ne kuma karo na biyu da ake balle katangar filin na Maracana, inda anan ne za’a buga wasan karshe a ranar 13 ga watan Yuli a gasar cin Kofin Duniya.

Talla

‘Yan kallo sanye da Jan riga sun kutsa ne a inda ‘Yan Jarida ke zama a filin wasan na Maracana da ke birnin Rio de Janiero, tare da balla gilashi da wani gefen katangar filin.

Yanzu haka ‘Yan sandan Brazil sun cafke mutane 85 kuma sun ba su wa’adi nan da sa’o’I 72 su fice daga kasar.

Magoya bayan Chile daga Latin Amurka suna kokarin shiga filin wasan ne domin kallon wasan da Chile ta doke Spain ci 2 da 0.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.