Brazil 2014

Uruguay ta doke Ingila

Luis Suarez yana murnar zira kwallo a ragar Ingila a gsar cin kofin duniya da ake gudanarwa a Brazil
Luis Suarez yana murnar zira kwallo a ragar Ingila a gsar cin kofin duniya da ake gudanarwa a Brazil REUTERS/Tony Gentile

Luis Suarez ya jefa kwallaye biyu a raga wanda ya taimakawa kasar shi Uruguay doke Ingila ci 2 da 1 a gasar cin kofin duniya zagayen farko da kasashen biyu suka fafata a Brazil.

Talla

Kocin Ingila Roy Hodgson yace ba zai yi murabus ba, bayan Ingila ta sake shan kashi ci 2 da1 a hannun Uruguay a rukuninsu na D.

A karawa ta farko, Ingila ta sha kashi ne a hannun Italiya, kuma wasu rahotanni na cewa hukumar kwallon Ingila ta fara nazarin raba gari da Roy Hodgson.

Ana saura minti 5 a kammala wasa ne Luis Suarez ya jefa kwallo ta biyu a ragar Ingila bayan Rooney ya farke kwallo ta farko.

Ko Ingila zata tsallake zuwa zagaye na biyu sai idan Italiya ta doke Costa Rica a yau Juma’a tare da doke Uruguay, sannan kuma idan har Ingila tana iya doke Costa Rica idan sun hadu.

Wannnan ne karon farko da ake wa Ingila barazanar ficewa gasar cin kofin duniya, tun a shekara ta 1958 da aka yi waje da kasar a zagayen farko.

Jaridun birtaniya sun yi sharhi ne a yau Juma’a akan Ingila bata iya tabuka komi idan ta hadu da manyan kasashe.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.