Brazil 2014

Argentina ta sha da kyar a hannun Iran

Lionel Messi na Argentina
Lionel Messi na Argentina REUTERS/Leonhard Foeger

Lionel Messi ya kwaci Argentina da kyar a hannun Iran ci 1-0 a fafatawar da suka yi a gasar cin kofin duniya da ake gudanarwa a Brazil. Yanzu Argentina ta tsallake zuwa zagaye na gaba da maki 6 kafin haduwarta da Najeriya.

Talla

Sai da aka kai dab da kammala wasan ne sannan Argentina ta samu ta jefa kwallo a ragar Iran. Amma Iran ta kai wa Argentina hare hare da dama.

Argentina ce yanzu ke jagorancin teburin rukunin F da maki 6 bayan ta doke Bosnia Hercegovina da Iran.

Argentina na iya jagorantar rukunin idan har aka tashi babu ci tsakanin Najeriya da Bosnia Hercegovina.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.