Kwallon kafa

Gasar cin kofin duniya; Faransa ta casa Switzeland ci 5 da 2

Dan wasan Faransa, lokacin da yake zura kwallo ta 2 a ragar Switzeland
Dan wasan Faransa, lokacin da yake zura kwallo ta 2 a ragar Switzeland REUTERS/Fabrizio Bensch

A ci gaba da wasanni a gasar cin kofin duniya da ake yi a kasar brazil, Faransa ta lallasa Switzeland ci 5 da 2. Mai koyar da ‘yan wasan kasar Switzeland Ottmar Hitzfeld, ya bayyana cewa kungiyar kwallon kafan kasar Faransa zata iya yin rawar gani matuka, a gasar ta cin kofin duniya.Hitzfeld ya fadi hakan ne bayan ‘yan wasan nashi sun sha kashi a hannun kasar Faransa.A nashi bangaren, mai koyar da ‘yan wasan na Faransa Didier Deschamps yace abinda ya ingiza ‘yan wasan nashi suka sami nasara a gasar cin kofin duniya da aka a shekarar 1998, yana tare da ‘yan wasan nashi a wannan karon.