Brazil 2014

Magoya bayan Brazil da Argentina sun yi gumurzu

magoya bayan Brazil suna gumurzu da magoya bayan Ingila
magoya bayan Brazil suna gumurzu da magoya bayan Ingila via Dailymail

An samu rikici tsakanin magoya bayan Brazil da Argentina a gasar cin kofin duniya da ake gudanarwar a Brazil, inda mutum guda ya samu mummunan rauni kuma ‘Yan sanda sun cafke mutum guda cikin masu rikicin. Rikicin ya faru ne a birnin Belo Horizente inda Argentina ta fafata da kasar Iran a yau Assabar.

Talla

Kafofin yada labaran Brazil sun ce rikicin ya barke ne bayan da wasu daga cikin magoya bayan kasashen biyu suka fara fashe fashen kwalabe.

Dubun dubatar ‘Yan kasar Argentina ne suka kai ziyara Brazil da suke makwabtaka, inda ake fargabar samun rikici daga masu tayar da kayar baya a tsakanin mutanen Argentina da Brazil da suka dade suna adawa da juna.

Yanzu haka mahukuntan Brazil sun tsaurara matakan tsaro a filayen wasannin da ake gudanar da gasar cin kofin duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.