Brazil 2014

Najeriya ta yi waje da Bosnia

Peter Odemwingie tare da abokan wasan shi na Najeriya suna murna bayan ya zira kwallo a ragar Bosnia a gasar cin kofin duniya da ake gudanarwa a Brazil.
Peter Odemwingie tare da abokan wasan shi na Najeriya suna murna bayan ya zira kwallo a ragar Bosnia a gasar cin kofin duniya da ake gudanarwa a Brazil. REUTERS/Eric Gaillard

Peter Odemwingie wanda ya jefa kwallo a raga ya taimakawa Najeriya yin waje da Bosnia-Hercegovina a gasar cin kofin duniya da ake gudanarwa a Brazil, nasarar da ta ba Najeriya kwarin gwiwar iya tsallakewa zuwa zagaye na gaba a karon farko.

Talla

Wannan ne karon farko da Najeriya ta samu nasara a gasar cin kofin duniya tun a gasar da aka gudanar a Faransa a shekarar 1998.

Miliyoyan ‘Yan Najeriya ne suka gudanar da biki cikinsu har da shugaban kasa Goodluck Jonathan saboda nasarar da Najeriya ta samu.

Shugaban wanda ya jagoranci biki da makarabbansa a fadar shugaban kasa ya yi wa ‘Yan wasan Super Eagles alkawalin goro idan har suka tabuka abin azo a gani a Brazil.

Argentina ce yanzu ke jagorancin rukunin F da maki 6 bayan ta doke Iran ci 1-0, yayin da Najeriya ke bi ma ta a matsayi na biyu da maki 4.

A ranar Alhamis ne Najeriya zata fafata da Argentina, kuma duk haduwar kasashen a gasar cin kofin duniya Najeriya ce ke shan kashi a hannun Argentina.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.