Algeria

Algeria ta mamayi Koriya ta Kudu da ci 4-2

Dan wasan Algeria, Madjid Bougherra
Dan wasan Algeria, Madjid Bougherra www.telegraph.co.uk

Kasar Algeria ta doke takwararta ta Koriya ta Kudu da ci 4-2 bayan karawar da bangarorin biyu suka yi a wasanninsu na biyu a gasra cin kofin duniya da ake yi a Brazil. Wannan nasara itace ta farko tun bayan wacce ta samu a shekarar 1982 a kan kasar Chile. 

Talla

Kasar Algeria itace kasa ta farko daga nahiyar Afrika, da ta fara samun nasarar zira kwallaye masu yawa a wannan gasa.

“Na sadaukar da wannan nasara ga dumbin magoya bayan Algeria wadanda suka yi dakon tsawon shekaru 32.” Mai horar da ‘yan wasan Algeria Vahid Halihodzic ya ce.

Tun kamin aje hutun rabin lokaci, Algeria ta zira kwallaye uku a ragar Koriya, wadanda Islam Slimani da Raficki Hallice da Abdelmoumene Djabou suka zira.

Wannan nasara na nufin Algeria na da maki uku, tana kuma sama da Rasha wacce ke da maki daya, yayin da Koriya ke da maki daya itama a rukuninsu na H.

Yanzu haka Koriya za ta buga wasanta na gaba ne da kasar Belgium wacce tuni ta samu damar tsallakawa zuwa zagaye na biyu.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.