Kwallon kafa

Faransa za ta fafata da Ecuardo

'Yan wasan PSG na Faransa suna murnar zira kwallo a raga
'Yan wasan PSG na Faransa suna murnar zira kwallo a raga

A yau Laraba Faransa za ta fafata da kasar Ecuardor a rukunin E, domin neman shiga zagaye na biyu a gasar cin kofin duniya.

Talla

Faransa dai na bukatar ko da kunnen doki ne a wannan wasa yayin da Ecuardo ke gaban Switzerland da yawan kwallaye.

Bangaren ‘yan wasan Didier Decshamp sun zira kwallaye guda takwas a wannan gasa ciki har da guda uku da Karim Benzema ya ci.

Yanzu haka ana sa ran Morgan Schneiderlin zai maye gurbin Yohan Cabaye da aka dakatar a wasan kasar na baya.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.