Kwallon kafa

FIFA na binciken Suarez kan zargin cizo

Dan wasan Uruguay, Luis Suarez
Dan wasan Uruguay, Luis Suarez REUTERS/Tony Gentile

Hukumar kwallon kafa ta duniya, FIFA ta ce ta kaddamar da bincike kan dan wasan kasar Uruguay Luis Suarez bisa zarginsa da ake yi da lafin yin cizo yayin karawarsu da Italiya. 

Talla

Kasar Uruguay ce ta lashe wasan da ci 1-0, amma zargin cizon Giorgio Chiellini da Suarez ya yi, ya mamaye batun ficewa kasar ta Italiya daga cikin gasar.

Wannan dai bashi ne karo na farko da aka taba samun Suarez da laifin yin cizo a lokacin wasa ba, a shekarar 2010 an haramta mai buga wasanni bakwai bayan da aka same shi da laifin cizon wani dan wasan kuniyar PSV a kasar Netherland a lokacin yana bugawa kungiyar Ajax.

Sannan a watan Aprilun bara aka sake haramta mai buga wasannin goma a gasar Premier ta ingila, bayan da aka sake samun shi da laifin cizon dan wasan Chelsea Branislav Ivanovic.

Shi dai Suarez yana buga wasa a kungiyar Liverpool a Ingina, muddin kuma aka same shi da laifi a wannan zargi da ake yi mai, hukumar ta FIFA za ta dauki tsatsauran mataki da zai hana ci gaba da buga gasar.

Yanzu haka Uruguay ta samu nasarar shiga zagaye na biyu a gasar.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.