Brazil 2014

Najeriya ta tsallake zagaye na gaba

Vincent Enyeama ya kabe kwallon Lionel Messi na Argentina
Vincent Enyeama ya kabe kwallon Lionel Messi na Argentina REUTERS/Stefano Rellandini

Argentina ta doke Najeriya ci 3 da 2, amma duk da haka Najeriya ta tsallake zuwa zagaye na gaba bayan Bosnia ta doke Iran ci 3 da 1 a rukuninsu na F. Wanna ne karon farko Najeriya ta samu kai wa ga zagaye na biyu a gasar cin kofin duniya tun a shekarar 1998.

Talla

Messi ne ya fara bude ragar Najeriya ana minti uku da fara wasa amma cikin minti guda Musa ya farke wa Najeriya kwallon tare da rama kwallo ta biyu da Messi ya jefa.

Ahmed Musa dan wasan Najeriya da ya rama kwallayen da Messi a karawa tsakaninin Argentina da Najeriya a Brazil
Ahmed Musa dan wasan Najeriya da ya rama kwallayen da Messi a karawa tsakaninin Argentina da Najeriya a Brazil REUTERS/Marko Djurica

Stephen Keshi ya jinjiniwa Messi musamman saboda kwallo ta biyu da ya zira daga harabar gidan Najeriya.

A zagaye na biyu Argentina za ta kara ne da Switzerland a filin Sao Pualo yayin da Najeriya za ta fafata da Faransa a wasansu na gaba.

A jiya Laraba Switzerland ta doke Honduras da ci 3-0, kuma Dan wasan Bayern Munich Xherdan Shaqiri ne ya jefa dukkanin kwallayen a raga yayin da Faransa da Ecuador suka ta shi canjaras.

Faransa ce ta jagoranci rukunin E yayin da Switzerland ke a matsayi na biyu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.