Brazil 2014

Suarez yana tsaka mai wuya

Cizon da Suarez ya yi dan wasan Italiya Giorgio Chiellini
Cizon da Suarez ya yi dan wasan Italiya Giorgio Chiellini Foto: Reuters

Yanzu haka ana dakun aji matakin da Hukumar kwallon Duniya FIFA zata dauka akan Luiz Suarez dan wasan Uraguay wanda ya kai wa dan wasan Italiya hari da cizo a gasar cin kofin duniya da ake gudanarwa a Brazil.

Talla

Tun a jiya ne dai kwamitin da’a na hukumar FIFA ya fara nazari game da hoton bidiyon da aka nuna Suarez ya ciji Giorgio Chiellini.

Suarez yanzu yana tsaka mai wuya, don yana na iya fuskantar hukunci mai tsauri,
Sau uku ke nan da Suarez ke yin cizo a filin kwallon, kuma a lokacin da ya ciji dan wasan Chelsea Ivanovic hukuncin haramcin wasanni 10 ne aka yanke masa.

Suarez ya sha suka a dandanlayen Intanet musamman a Facebook da Twitter. Wasu da dama suna kira ne ga FIFA ta dauki mataki mai tsauri.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.