Brazil 2014

An yi wa ‘Yan wasan Ghana guzurin Kudi

'Yan wasan Ghana John Boye, Andre Ayew, Jonathan Mensah, Christian Atsu, Asamoah Gyan da Mubarak Wakaso
'Yan wasan Ghana John Boye, Andre Ayew, Jonathan Mensah, Christian Atsu, Asamoah Gyan da Mubarak Wakaso REUTERS/Mike Blake

Rahotanni sun ce akwai damen kudi sama Dala Miliyan uku da gwamnatin Ghana ta aika wa ‘Yan wasan Black Stars domin karawa ‘Yan wasan gwarin gwiwa kafin su kara da Portugal a yau Alhamis.

Talla

Ghana dai tana bukatar samun nasara a karawarta da Portugal kafin ta samu hurumin tsallakewa zuwa zagaye na gaba. Rahotanni sun ce akwai bore da wasu ‘Yan wasan suka soma saboda rashin binyansu kudadensu na lada.

Irin wannan matsalar ce ta shafi ‘Yan wasan Kamaru wadanda suka fara ficewa Brazil tun a tashin farkodaga cikin kasashen Afrika da ke fafatawa a gasar cin kofin duniya.

Yanzu kasashen Latin Amurka ne suka fi yawa a gasar bayan an yi waje da manyan kasashen Turai da Asiya da wasu kasashen Afrika tun a zagayen farko.

Yanzu akwai Brazil da ke daukar nauyin gasar zuwa Mexico da Argentina da Chile da Colombia da Uraguay, saboda a yankinsu ne ake gudanar da gasar.

Kuma yanzu dubban magoya bayan kasashen a Brazil  shi ne babbar barazana ga jami’an tsaron kasar saboda yadda suka dauki kwallon kafa kamar ibada.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.