Brazil 2014

Algeria ta tsallake zuwa zagaye na biyu

'Yan kasar Algeria suna bikin samun nasara a gasar cin kofin duniya da ake gudanarwa a Brazil
'Yan kasar Algeria suna bikin samun nasara a gasar cin kofin duniya da ake gudanarwa a Brazil REUTERS/Louafi Larbi

Belgium da Algeria sun tsallake zuwa zagaye na biyu, wadanda suka kora Rasha da Korea ta Kudu zuwa gida a rukuninsu na H. Wannan ne karon farko da kasar Algeria ta tsallake zuwa zagaye na biyu a gasar cin kofin duniya bayan ta yi kunnen doki da Rasha a jiya Alhamis.

Talla

Kasashen Nahiyar Afrika yanzu guda biyu ne suka tsallake zuwa zagaye na biyu da Najeriya da Algeria bayan an yi waje da cote d’Voire da Kamaru da kuma Ghana.

Kasar Belgium ta doke Korea ta kudu ne ci 1 da 0, wanda ya ba Belgium nasarar jagorantar rukuninsu na H da maki 9.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.