Brazil 2014

FIFA ta dakatar da Suarez

Suárez ya dafe baki bayan ya ciji dan wasan Italiya a gasar cin kofin duniya a Brazil
Suárez ya dafe baki bayan ya ciji dan wasan Italiya a gasar cin kofin duniya a Brazil REUTERS/Tony Gentile/Files

Hukumar FIFA da ke kula da kwallon kafa a duniya ta dakatar da Luiz Suarez na tsawon watanni 4, bayan ya kai wa dan wasan Italiya Giorgio Chiellini hari da cijo a lokacin da suke fafatawa a gasar cin kofin duniya a Brazil.

Talla

Wannan dai shi ne hukunci mafi tsauri da hukumar FIFA ta yankewa dan wasa.
Haka kuma An ci tarar Suarez kudi dalar Amurka 112,000.

Hukumar FIFA ta yanke hukuncin ne bayan Kwamitin da’a ya kammala bincike. Kuma shugaban kwamitin Claudio Sulser yace ba za su amince da irin wannan tabi’ar cizo ta Suarez ba a filin wasa.

Wannan ne karo na uku da ake daukar mataki akan Suarez game da cijo a filin wasa, tun lokacin da yana taka kwallo a Holland a 2010 har zuwansa Liverpool inda ya dankarawa dan wasan Chelsea Branislav Ivanovic hakora a bara.

Suarez yanzu zai kauracewa buga kwallon kafa daga nan har zuwa watan Oktoba, a yayin da kuma kasar shi Uruguay a yayin da a gobe Assabar ne Uruguay zata kara da Colombia ba tare da Suarez ba wanda ya taimakawa kasar tsallakewa zuwa zagaye na biyu.

Jaridun kasar Birtaniya inda Suarez ke taka kwallo da kungiyar Liverpool sun yaba da wannan matakin da aka dauka akan Suarez, wanda hakan ya shafi rayuwarsa a Liverpool kuma zai dakatar da farautar da Barcelona ke yi wa Dan wasan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI