Brazil 2014

An kori Ghana da Portugal a Brazil

Mai tsaron gidan Ghana Fatau Dauda yana kokarin kabe kwallon Cristiano Ronaldo a gasar cin kofin duniya
Mai tsaron gidan Ghana Fatau Dauda yana kokarin kabe kwallon Cristiano Ronaldo a gasar cin kofin duniya REUTERS/David Gray

Kasashen Ghana da Portugal sun fice gasar cin kofin Duniya duk da Portugal ta doke Ghana ci 2 da 1 a jiya Alhamis, Jamus da Amurka ne suka tsallake a rukuninsu na G. Cristiano Ronaldo zakaran kwallon duniya ya bi sahun manyan zaratan ‘Yan kwallon Turai da aka yi waje da su a gasar tun a tashin farko.

Talla

A tawagar Ghana kawai sabani da aka samu tsakanin ‘Yan wasa da shugabanninsu a Brazil.

An dakatar Sulley Muntari da Kevin-Prince Boateng kuma hukumar kwallon Ghana tace Muntari ya kai wa wani jami’in hukumar ne bugu yayin da kuma Boateng ya zagi mai horar da ‘Yan wasa Kwesi Appiah.

Jamus ce dai ta jagoranci rukunin G da maki 7, bayan ta doke Amurka ci 1 da 0.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.