Brazil 2014

An tube Ministan wasannin Ghana

'Yan wasan Ghana a lokacin da suka sha kashi a karawarsu da Portugal
'Yan wasan Ghana a lokacin da suka sha kashi a karawarsu da Portugal REUTERS/Dylan Martinez

Ministan Wasanni a kasar Ghana da mataimakinsa sun yi murabus daga mikaminsu bayan an yi waje ‘Yan wasan Black Stars tun a zagayen farko a gasar cin kofin duniya da ake gudanarwa a Brazil. Akwai sabani da aka samu tsakanin wasu ‘Yan wasan Ghana da kuma shugabaninsu da suka je Brazil.

Talla

Sanarwar yin murabus din ta fito ne daga ofishin Shugaban Ghana John Dramani Mahama, kuma a ciki an mayar da Ministan Wasanni Elvis Afriyie-Ankrah zuwa karamin Minista a fadar shugaban kasa.

An sauya Mataimakinsa Joseph Yammin zuwa karamin Ministan lardin Ashanti.

Tun a zagayen farko ne aka yi waje da Ghana a rukuninsu na G da ya hada manyan kasashe Portugal da Jamus da Amurka, duk da zaratan ‘Yan wasan kasar da suka hada da Michael Essien da Asamoah Gyan

A tawagar Ghana kawai sabani da aka samu tsakanin ‘Yan wasa da shugabanninsu a Brazil.

An dakatar Sulley Muntari da Kevin-Prince Boateng kuma hukumar kwallon Ghana tace Muntari ya kai wa wani jami’in hukumar ne bugu yayin da kuma Boateng ya zagi mai horar da ‘Yan wasa Kwesi Appiah.

Jamus ce dai ta jagoranci rukunin G da maki 7, bayan ta doke Amurka ci 1 da 0.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.