Wasanni

Nigeria za ta kara da Faransa a gasar neman Kofin Duniya

Alamar hukumar FIFA Brazil 2014
Alamar hukumar FIFA Brazil 2014

A marecen yau ne za a fayyace makomar sauran kasashen Afirka biyu da ke halartar gasar neman kofin duniya, wato Najeriya da kuma Aljeriya.

Talla

Da farko dai za a kara ne tsakanin Najeriya da kasar Faransa da misalin karfe biyar na marece agogon Najeriya, yayin da Aljeriya za ta fafata da kasar Jamus da misalin karfe tara.

Daga cikin wadannan kasashen biyu na Afirka wato Najeriya da kuma Algeriya, ba wanda ya taba zuwa zagayen da ke biyewa na kusa na da karshe wato quarter finals a wannan gasa ta neman kofin duniya, idan kuma suka yi nasara, to ana iya cewa sun kafa tarihi bayan wanda kasashen Kamaru, Senegal da kuma Ghana suka kafa a cikin shekarun da suka gabata a wannan gasa.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.