Brazil

An rada wa wani Yaro sunayen ‘Yan wasa shida

Wani Yaro Dan kasar Brazil da aka radawa sunan 'Yan wasan Faransa Zidane Thierry Henry Barthez
Wani Yaro Dan kasar Brazil da aka radawa sunan 'Yan wasan Faransa Zidane Thierry Henry Barthez features.insing.com

A kasar Brazil an radawa wani Yaro sunayen tsoffin ‘Yan wasan Faransa guda hudu da wasu ‘Yan Brazil guda biyu. Ana kiran yaron ne da sunan Zinedine Yazid Zidane Thierry Henry Barthez Eric Felipe Silva Santos.

Talla

Mahaifin yaron mai suna Petrucio Santos, ya shaidawa wata kafar yada labarai ta G1 cewa tsabagen son ‘Yan wasan Faransa ne ya sa ya radawa yaron shi sunayen tsoffin ‘Yan wasan kasar da suka doke Brazil a gasar cin kofin duniya da aka gudanar a 2006.

Yaron mai shekaru bakwai na haihuwa, an fi sanin shi ne da sunan Zidane amma yace bai san dukkanin ‘Yan wasan da ya ke amfani da sunayensu ba.

Zidane da Henry da Barthez dukkaninsu ‘Yan wasan Faransa ne suka haska a gasar cin kofin Duniya a lokacin da Faransa ta doke Brazil a 2006.

Eric kuma sunan tsohon dan wasan Manchester United ne dan kasar Faransa Eric Cantona, yayin da kuma Felipe sunan mai horar da ‘Yan wasan Brazil ne na yanzu Luiz Felipe Scolari.

Silva Santos sunan asali ne na Yaron da suke da tushe a garin Maceio babban birnin Jahar Alagoas a Brazil.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.