Tennis

Bouchard da Petra sun kai zagayen karshe

Petra Kvitova 'Yar kasar Czech a lokacin da take karawa da Dushevina ta Rasha
Petra Kvitova 'Yar kasar Czech a lokacin da take karawa da Dushevina ta Rasha Reuters

Eugenie Bouchard da Petra Kvitova ne zasu buga wasan karshe a bangaren mata a gasar Wimbledon da ake gudanarwa a Birtaniya. Eugenie Bouchard ita ce ‘Yar wasan Tennis ta farko daga kasar Canada da ta kai ga zagayen karshe a babbar gasar Tennis bayan ta doke Simona Halep ta Romania a zagayen dab da na karshe.

Talla

Petra Kvitova kuma da ta taba lashe kofin gasar a 2011 ta tsallake ne bayan ta doke Lucie Safarova takwararta ta Jamhuriyar Czech.

A gobe Assabar ne Jaruman na Tennis zasu kara da juna.

A bangaren Maza kuma a yau Juma’a ne za’a kara tsakanin Novak Djokovic da dan wasan Belgium Grigor Dimitrov. Roger Federer zai kara ne da Milos Raonic

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.