Brazil 2014

Messi ya tausaya wa Neymar

Hoton da Messi ya sanya a shafin shi na Facebook yana tare da Neymar suna sanye da rigar Barcelona
Hoton da Messi ya sanya a shafin shi na Facebook yana tare da Neymar suna sanye da rigar Barcelona Leo Facebook

Lionel Messi na Argentina wanda ya lashe kyautar gwarzon duniya sau hudu ya tausayawa Neymar abokin wasan shi a Barcelona tare da yi masa fatar samun sauki da wuri bayan dan wasan na Brazil ya samu rauni a lokacin da suke fafatawa da Colombia a gasar cin kofin Duniya.

Talla

Messi ya aiko da sakon fatar alheri ne ga Neymar a shafin shi na Facebook tare da saka hoton shi da Neymar sanye da rigar kungiyar Barcelona da suke taka leda.

Neymar kwance a makara a lokacin da ya samu rauni a wasan Brazil da colombia
Neymar kwance a makara a lokacin da ya samu rauni a wasan Brazil da colombia Foto: Reuters

Neymar ya samu rauni ne a bayansa sakamakon bigewar da dan wasan Colombia Juan Camili Zuniga ya yi ma shi ana dab da kammala wasa tsakanin Brazil da Colombia.

Yanzu Neymar ba da shi Brazil zata buga sauran wasanninta ba da suka rage a gasar cin kofin duniya bayan Likitoci sun ce  zai kwashe makwanni yana jinya,

Brazil  ta doke Colombia ne a wasan ci 2 da 1.

Idan an jima ne Argentina zata kara da Belgium a zagayen Kwata Fainal kuma Messi yana fatar kada annobar da ta fada wa Neymar ta same shi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.