Wasanni

Brazil da Jamus, Holland da Argentina a zagayen kusa da na karshe

'yan wasan Brazil, Jamus, Holland da Argentina
'yan wasan Brazil, Jamus, Holland da Argentina

A kasar Brazil ana ci gaba da gudanar da gasar neman kofin duniya na kwallon kafa, kuma yanzu haka kasashen Argentina, Brazil, Jamus da kuma Netherlands wato Holland ne suka rage a gasan inda za su kara a zagayen kusa da na karshe, bayan da suka yi nasara a wasannin da suka buga a karshen makon da ya gabata.

Talla

Kasar Jamus dai, ta doke Faransa ne ci 1 da nema, sai Brazil da ta doke Colombia ci 2 da 1, Argentina ta yi nasara ne a kan kasar Belgium ci 1 da nema, yayin da Netherlands ta yi kare jini biri jini da kasar Costa Rica har sai da aka je bugun daga kai sai mai tsaron gida, inda suka tashi wasa ci 4 da 3 wato Netherlands na da nasara.

A gobe talata ne dai za a kara a zagayen kusa da na karshe tsakanin Brazil da kuma Jamus a filin wasa na Belo Horizonte, sai kuma Holland wadda za ta kara da Argentina a jibi laraba a filin wasa na Sao Paulo.

Uku daga cikin wadannan kasashe sun taba daukar kofin na duniya, wato Brazil wadda ta dauki kofin har sau 5, 1958, 1962, 1970, 1994 da kuma shekara ta 2002, ita ma Jamus ta taba daukar wannan kofi har sau uku, wato 1954, 1974 da kuma 1990, yayin da Argentina ta dauki kofin na duniya har sau biyu, 1978 da kuma 1986.

Ita kuwa kasar Netherlands ko kuma Holland har yanzu ba ta samu nasarar daukar wannan kofi ba, to sai dai ta je zagayen karshe na gasar har sau uku, kuma a wannan karo ake ci gaba da karawa da ita.

To sai dai kasar Brazil za ta buga wannan wasa na gobe talata ne ba tare da shahrarren dan wasanta ba wato Thiago Silva, wanda aka bai wa katin gargadi har sau biyu, duk da cewa Brazil ta shigar da kara a gaban hukumar Fifa domin nuna rashin amincewa da katin da aka bai wa Silva a karawarsu da Colombia.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.