Wasanni

Zango na uku a gasar tseren kekuna na Tour de France

Philippe Gilbert, wanda ya shahrara a gasar Tour de France
Philippe Gilbert, wanda ya shahrara a gasar Tour de France AFP PHOTO / PASCAL GUYOT

A wannan talata an shiga rana ta 4 a ci gaba da fafatawa a gasar tseren kekuna ta Tour de France, inda 'yan tsere daga kasashe daban daban na duniya suka za su yi tafiyar kilomita 163 daga Ingila zuwa Faransa. 

Talla

A jiya litinin Marcel Kittel dan asalin kasar Jamus ne ya yi nasara a zango na uku na wannan gasa mai tazarar kilomita 155 daga Cambridge zuwa London a kasar Ingila, kuma wannan ne karo na biyu da ya samu galaba duk da cewa karo na uku kenan da ya shiga gasar ta Tour de France.

A ranar lahadi da ta gabata kuwa, zakaran tseren kekuna na kasar Italia Vincenzo Nibali ya zama zakara a zango na biyu na gasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.