Kwallon kafa

FIFA: Jamus ce gwanin tamola a duniya

'Yan wasan kasar Jamus suna bikin lashe kofin gasar cin kofin duniya a Brazil
'Yan wasan kasar Jamus suna bikin lashe kofin gasar cin kofin duniya a Brazil REUTERS/Michael Dalder

Kasar Jamus yanzu ke jagorancin teburin ajin matsayin kasashen duniya na hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA a karon farko tsawon shekaru 20 bayan kammala gasar cin kofin duniya da kasar ta lashe a Brazil.

Talla

Jamus ta karbe matsayin ne bayan ta doke Argentina ci 1 da 0 a gasar cin kofin duniya da aka kammala a kasar Brazil.

Kasar Argentina ce a matsayi na biyu, sai Holland a matsayi na uku kamar yadda ta zo na uku a gasar cin kofin duniya a Brazil.

Kasar Spain da ta kwashe lokaci tana jagorancin teburin bayan ta lashe kofin duniya a Afrika ta kudu, yanzu ta koma ne a matsayi na 8.

Daga Matsayi na farko zuwa 20 babu wata kasa daga Afrika.

Jerin Matsayin kasashen duniya a fagen kwallon Kafa

1. Germany (+1)

2. Argentina (+3)

3. Netherlands (+12)

4. Colombia (+4)

5. Belgium (+6)

6. Uruguay (+1)

7. Brazil (-4)

8. Spain (-7)

9. Switzerland (-3)

10. France (+7)

11. Portugal (-7)

12. Chile (+2)

13. Greece (-1)

14. Italy (-5)

15. USA (-2)

16. Costa Rica (+12)

17. Croatia (+1)

18. Mexico (+2)

19. Bosnia and Hercegovina (+2)

20. England (-10)
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.