Isa ga babban shafi
Premier League

Van Gaal ya fara aiki a Manchester United

Louis van Gaal, Sabon Kocin Manchester United
Louis van Gaal, Sabon Kocin Manchester United eurosport.com

Luis Van Gaal ya fara aiki a Manchester United a jiya Laraba bayan ya jagoranci tawagar Holland a gasar cin kofin duniya a Brazil. A yau Alhamis ne zai fara ganawa da ‘Yan jarida a matsayin kocin Manchester United.

Talla

Babban kalubalen da ke gaban Van Gaal shi ne farfado da matsayin United a Turai, bayan an kammala kaka tana matsayi na 7 a teburin Premier.

Van Gaal mai shekaru 62 shi ne ya gaji David Moyes da ya dushe martabar United bayan ya gaji Alex Farguson.

Van Gaal zai yi aiki ne tare da Ryan Giggs a mtsayin mataimakinsa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.