Wasanni

An bude wasannin Commonwealth

Wasannin kasashen renon Ingila a Scotland
Wasannin kasashen renon Ingila a Scotland REUTERS/Russell

An bude wasannin kasashen renon ingila, a jiya Laraba, kuma Sarauniyar Ingila Queen Elizebeth ce ta bude wasannin karo na 20 a birnin Glasgow kasar Scotland. ‘Yan wasa 4,500 daga kasashe 71 ne suka shiga wasanni 17 da za’a kwashe kwanaki 11 ana gudanarwa.A yau Alhamis ne aka fara wasannin gadan gadan.