Ingila

Rooney ya cancanta ya zama Kaftin-Ferdinand

Dan wasan Ingila Wayne Rooney
Dan wasan Ingila Wayne Rooney

Tsohon dan wasan Manchester United Rio Ferdinand yace Wayne Rooney ya cancanta ya zama Kaftin na Ingila bayan Steven Gerrard ya yi ritaya daga bugawa kasar shi wasa. Ferdinand yace Rooney ya fi cancanta fiye da sauran ‘Yan wasan Ingila da ake hasashen zasu gaji Gerrard.

Talla

Ana dai hasashen Roy Hodgson zai nada sabon kaftin tsakanin Rooney da Gary Cahill da kuma mai tsaron gida Joe Hart.

Amma Fardinand wanda ya kwashe tsawon watanni 13 yana jagorantar Ingila yace Rooney ya fi dacewa ya gaji Gerrard saboda kwarewarsa.

A shekarar 2003 ne Rooney ya fara haskawa a tawagar Ingila, kuma tun lokacin ya zirara kallaye 40 a raga.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.