Wasanni

Kwamitin gudanarwa na NFF ya yi watsi da matakin tube Maigari

Tubabben shugaban hukumar kwallon Najeriya Aminu Maigari
Tubabben shugaban hukumar kwallon Najeriya Aminu Maigari Kickoff.com

A Najeriya mafi yawa daga cikin mambobi da suka halarci taron koli na hukumar kwallon kafar kasar NFF, sun yi watsi da matakin da aka dauka na korar Aminu Maigari daga matsayinsa na shugaban hukumar.

Talla

A lokacin wannan zama, mambobi 26 daga cikin 44 na NFF ne suka jaddada goyon bayansu ga Maigari, inda suka ce ba a bi ka’idojin da suka dace wajen tube shi daga kan mukaminsa a cikin makon jiya ba.
Wannan dai mataki dai zai iya kara zafafa halin da hukumar kwallon kafar kasar ta fada har ma hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA ta dauki matakin dakatar da Najeriya daga shiga dukkanin wasannin da take shiryawa.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.