Kwallon Kafa

Liverpool ta doke Manchester City

Yaya Toure ya barar da Fanalti a wasan sada zumunci da Manchester City ta fafata da Liverpool
Yaya Toure ya barar da Fanalti a wasan sada zumunci da Manchester City ta fafata da Liverpool Reuters

Kungiyar Liverpool ta samu sa’ar Manchester city ci 3 da 2 a bugun Fanalti bayan manyan kungiyoyin biyu na Ingila sun tashi ci 2 da 2 a wasan sada zumunci da suka fafata a birnin New York na Amurka. Mai tsaron gidan Liverpool ne ya kwaci kungiyar inda ya kabe kwallaye biyu.

Talla

Aleksandar Kolarov da da Yaya Toure da Navas suka barar wa City kwallayenta a ragar Liverpool a bugun Fanalti.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.