Wasanni

An kammala wasannin kasashe renon Ingila

Wasannin kasashen Commonwealth a Glasgow
Wasannin kasashen Commonwealth a Glasgow REUTERS

A yammacin jiya ne aka rufe wasannin kasashe renon Ingila karo na 20 a birnin Glasgow na kasar Scotland, inda ‘yan wasa daga kasashe 71 suka share tsawon kwanaki 11 suna fafatawa a wasanni daban daban har guda 17.

Talla

An dai gudanar da gagarumin biki domin rufe wasannin a karkashin jagorancin shugaban hukumar shirya wadannan wasanni Mike Hooper.

Ko shakka babu dai kasar Ingila ce ta fi kowace kasa samun kyaututuka, inda ta tashi da guda 174, sai Australiya a matsayin ta 2 da kyaututuka 137, yayin da Afirka Ta Kudu ta zo a matsayin ta 7 da nata kyaututuka 40, sai Najeriya a matsayin ta 8 da nata kyaututukan dangin zinari, azurfa da kuma tagulla guda 36.

An dai zabi birnin Gold Coast na kasar Australiya a matsayin wanda zai karbi wasannin a shekara ta 2018.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI