Xavi ya yi wa Spain ritaya
Wallafawa ranar:
Fitattacen Dan wasan Spain Xavi Hernandez malamin raba kwallo a Barcelona ya bayyana yin ritaya daga bugawa kasar shi kwallo, bayan ya taimakawa Spain lashe kofin Turai guda biyu tare da lashe kofin duniya a kasar Afrika ta kudu a 2010. Xavi mai shekaru 34 ya shaidawa manema labarai cewa lokaci ne ya yi da zai kawo karshen bugawa kasar shi wasa.
Ana ta rade radin dan wasan zai fice Barcelona a bana amma Xavi yace zai ci gaba da taka leda da kungiyar da ta rene shi tun kuriciyarsa.
Xavi yana cikin tawagar Spain da aka yi waje da su tun a tashin farko a gasar cin kofin duniya da aka gudanar a kasar Brazil bayan sun lashe kofin a Afrika ta kudu.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu