La liga

Benzema ya sabunta kwantaraginsa a Madrid

Karim Benzema na Real Madrid
Karim Benzema na Real Madrid REUTERS/Michael Dalder

Dan wasan Faransa Karim Benzema ya sabunta kwantaraginsa da kungiyar Real Madrid, wanda ya kawo karshen jita jitar da ke yi akan makomarsa a kungiyar da ke rike da kofin zakarun Turai. Real Madrid ta wallafa a shafinta na intanet cewa Benzema ya kulla sabuwar yarjejeniya ne ta shekaru 5, daga nan har zuwa shekara ta 2019.