Real Madrid ta lashe Super Cup
Wallafawa ranar:
Real Madrid da ta lashe kofin zakarun Turai ta sake lashe kofin Super na Turai bayan ta doke Sevilla ci 2 da 0. Cristiano Ronaldo ne ya zirara dukkanin kwallaye biyu a ragar Sevilla da ta lashe kofin Europa League.
Ana fafata neman lashe kofin Super ne tsakanin Kungiyar da ta lashe kofin Zakarun Turai da kofin Europa League manyan gasanni guda biyu a Turai.
Ronaldo ya buga wasan ne tare da Benzema da Gareth Bale da kuma sabbin ‘Yan wasan da Real Madrid ta sayo a kasuwa a bana Toni Kroos da James Rodriguez wanda wannan zubin ‘Yan wasan a kungiya guda shi ne mafi tsada a tarihin kwallon kafa
Jimillar kudin ‘Yan wasan sun kai sama da euro Miliyan 310.
Wannan ne karo na biyu da Real Madrid ta lashe kofin na Super bayan lashe kofin a 2002.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu