Premier League

Rooney ya zama Kaftin na Manchester

Wayne Rooney na Manchester United
Wayne Rooney na Manchester United REUTERS/Phil Noble

Louis van Gaal, ya nada Wayne rooney a matsayin kaftin na Manchester United, bayan United ta doke Valencia ci 2 da 1 a wasan sada zumunci da suka fafata a filin wasa na Old Trafford. Roonay ya gaji Vidic ne wanda ya koma Inter Milan.

Talla

Van Gaal yace Rooney ya cancanci ya jagoranci Manchester bayan ya yaba masa.
Rooney kuma wanda a baya ya so ficewa Manchester ya gode wa Van Gaal ga sabon mukamin inda kuma ake hasashen zai zama kaftin na Ingila bayan Steven Gerrard ya yi murabus.

A jiya Talata kuma kungiyar Chelsea ta doke Real Sociedad ci 2-0 kuma sabon dan wasan kungiyar ne Diego Costa ya jefa kwallaye biyu a raga.

Kungiyar Liverpool kuma ta kammala cininkin Alberto Moreno daga Sevilla.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.