Kwallon Kafa
Suarez yana jiran tsammani
Wallafawa ranar:
Dan wasan Uruguay Luis Suarez na Barcelona zai saurari sakamakon koken da ya shigar a kotun Wasanni ta duniya a yau Alhamis game da hukuncin haramcin shiga sha’anin kwallo na tsawon watanni hudu da hukumar FIFA ta dauka akansa saboda ya ciji Giorgio Chiellini na Italiya a lokacin da ake gudanar da gasar cin kofin duniya a Brazil.
Talla
Suarez yana neman a rage masa hukuncin bayan ya shigar da kokensa a makon jiya.
A yau ne kuma kotun tace zata bayyana hukuncin da ta dauka da misalin karfe 1 agogon GMT.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu