CAF

Ebola: CAF ta dauke wasanni a Liberia da Saliyo

Issa Hayatou Shugaban hukumar kwallon Afrika
Issa Hayatou Shugaban hukumar kwallon Afrika CAF

Hukumar kwallon Afrika CAF ta dauke wasanninta na neman shiga gasar cin kofin Afrika a kasashen Guinea da Liberia da Saliyo saboda barazanar Ebola da ke kisan jama’a a kasashen. CAF ta bukaci kasashen uku su yi shawarar kasashen da suke son a dawo da wasanninsu.

Talla

Kasar Ghana ta amince ta karbi bakuncin Saliyo a fafatawar da zata yi da Jamhuriyyar Congo. Tuni Liberia ta haramta wasannin kwallo a kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI