Kwallon Kafa

Suarez ya fara horo a Barcelona

Suarez yana horo a sabuwar kungiyar shi Barcelona bayan ya samu sassaucin hukuncin cizo
Suarez yana horo a sabuwar kungiyar shi Barcelona bayan ya samu sassaucin hukuncin cizo REUTERS/Gustau Nacarino

Luis Suarez ya fara horo a Barcelona a yau Juma’a bayan kotun daukaka kara ta wasanni ta yi ma sa sassauci ga hukuncin da FIFA ta yanke masa na haramcin shiga sha’anin kwallo na tsawon wata hudu saboda ya ciji dan wasan Italiya Giorgio Chiellini a gasar cin kofin duniya da aka gudanar a kasar Brazil.

Talla

A shafin intanet na Barcelona, Kungiyar tace Suarez zai fara horo da sanyin safiyar Juma’a bayan sassauta masa hukuncin FIFA.

Kungiyar kuma tace a ranar Litinin ne zata gabatar da dan wasan ga magoya bayanta a Camp Nou lokacin da kungiyar zata buga wasan zumunci domin lashe kofin Joan Gamper.

Kotun daukaka kara ta wasanni tace Suarez na da damar buga wa kasarsa Uraguy wasannin sada zumunci, sannan zai iya yin horo da sabuwar kungiyar shi Barcelona.

Rahotanni sun ce Suarez ya dade yana horo shi kadai a yankin Catolinia a Barcelona tun yanke ma sa hukucin haramcin wasanni.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI