Premier League

Balotelli zai koma Liverpool

Mario Balotelli na AC Milan
Mario Balotelli na AC Milan REUTERS/Giorgio Perottino

Kungiyar Liverpool na dab da karbo Mario Balotelli daga AC Milan, kuma rahotanni sun ce a yau Juma’a za’a kammala cinikin dan wasan tsakanin kungiyoyin biyu. Rahotanni daga Italiya da Ingila sun ce Liverpool ta zubawa Balotelli kudi euro Miliyan 20, kuma tun a jiya Alhamis shafin Intanet na AC Milan ya wallafa cewa Balotelli ya yi wa abokan wasan shi ban kwana a San Siro bayan kammala horo a lokacin da ya ke jiran tsammani.

Talla

Idan dai har cinikin dan wasan mai shekaru 24 ya tabbata, Balotelli zai iya haskawa a fafatawar da Liverpool zata yi da tsohuwar kungiyar shi Manchester City a ranar Litinin.

Liverpool tana son ta maye gurbin Luis Suarez day a koma Barcelona.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI