Kwallon Kafa

Ban nemi ficewa Madrid ba- Di Maria

Angel Di Maria na Argentina
Angel Di Maria na Argentina manutd.com

Dan wasan Argentina Angel Di Maria yace bai nemi ficewa Real Madrid ba bayan Manchester United ta kammala cinikinsa akan kudi Dala Miliyan 98. Dan wasan ya shaidawa Jaridar Marca a cikin wata wasika cewa ba da son ransa ba ya fice Real Madrid.

Talla

Tun kafin kammala cinikin Di Maria, Kocin Real Carlo Ancelotti ya yi ikirarin cewa dan wasan ya nemi ya fice daga Kungiyar, ikirarin da kuma dan wasan ya musanta.

Dan wasan yace shugabannin Real Madrid sun fadi abubuwa da dama akan makomarsa.

Di Maria dai ya fara fuskantar kalubale ne a Real Madrid bayan kungiyar ta sayo James Rodriguez da Toni Kroos da zasu kwace masa wuri.

Dan wasan dai ya bayyana fatar samun makoma mai kyau a Manchester United da ta ware makudan kudade ta karbo shi daga Real Madrid.

Wannan kuma na zuwa ne a yayin da Kungiyar Milton da ke taka kwallo a mataki na uku a Ingila ta lallasa Manchester United ci 4 da 0 a gasar League Cup, kuma Manchester ta fice gasar bayan ta samu maki 1 kacal a wasanni biyu da Van Gaal ya fara jagorantar kungiyar a Premiership.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.