Cristiano ne gwarzon Turai
Wallafawa ranar:
Cristiano Ronaldo na Real Madrid aka ba gwarzon dan wasan Turai, bayan ya samu rinjayen kuri’un ‘Yan jarida da ke zaben fiye da Manuel Neuer Arjen Robben. Ronaldo ya gaji Franck Ribery na Faransa ne da ya lashe kyautar a bara.
Bayan karbar kyautar ta Ballon d'Or daga hannun Michel Platini shugaban hukumar kwallon Turai, Ronaldo yace yana cike da farin ciki tare da godewa abokan wasan shi a Real Madrid.
Duk da dai babu wata rawa da Ronaldo ya taka a gasar cin kofin duniya da aka gudanar a Brazil amma shi ya jagoranci Real Madrid ga nasarar lashe kofin zakarun Turai karo na 10, tare da jefa kwallaye 17 a gasar.
A bangaren mata kuma Nadine Kessler ce ta zama jaruma a Turai bayan ta jagoranci Wolfsburg ga nasarar lashe kofin zakarun Turai na mata.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu