Champions League

An hada Real da Liverpool a rukuni guda

Kungiyar Real Madrid da ke rike da kofin zakarun Turai an hada ta rukuni daya da Liverpool yayin da kuma aka hada Barcelona rukuni guda Paris Saint-Germain a bikin da UEFA ta gudanar a birnin Monaco inda aka hada rukunin kungiyoyin da zasu kece raini da juna a gasar zakarun Turai zagayen farko.

Rukunin Kungiyoyin da aka hada wasa a zagayen Farko a gasar Zakarun Turai a Monaco
Rukunin Kungiyoyin da aka hada wasa a zagayen Farko a gasar Zakarun Turai a Monaco REUTERS/Eric Gaillard
Talla

Rukunin da dai ya ja hankali shi ne rukunin B inda aka hada Real Madrid da ta lashe kofin sau 10 wasa da Liverpool da ta lashe kofin sau biyar, duk da cewa an kwashe shekaru biyar ana gasar ba tare da Liverpool ba .

Ana ganin dai Real da Liverpool zasu iya tsallakewa a rukunin idan har suka iya doke sauran kungiyoyin da aka hada su a rukunin B Ludogorets ta Bulgaria da kuma FC Basel ta Switzerland da ta yi waje da Manchester United shekaru uku da suka gabata.

Rukunin A kuma an hada Atletico Madrid ne tare da Juventus da Olympiacos da Malmo.

Rukunin C kuma aka hada Benfica da Zenit st Petersburg da Monaco.

An hada kuma Arsenal ne a rukunin D tare da Borussia Dortmund da Galatasaray da kuma Anderlecht.

Rukunin da kuma ya dauki hankali shi ne rukunin E da aka hada Bayern Munich da Manchester City da Roma da kuma CSKA Moscow.

Wannan ne karo na uku a shekaru hudu da Bayern Munich da Manchester City ke haduwa a zagayen farko.

A rukunin F, an hada Barcelona ne da Paris Saint-Germain da Ajax da kuma Apoel ta Cyprus.

Amma a rukunin G ana ganin Chelsea ta samu sassauci bayan an hada ta wasa a rukunin tare da Schalke 04 da Sporting Lisbon da Maribor ta Slovenia.

Rukunin karshe na H an hada FC Porto da Shakhtar Donetsk da Athletic Bilbao da kuma Bate Barisov.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI