Wasanni

Wasannin share fage na shiga gasar neman kofin Afirka

Mai horas da 'yan wasan Najeriya Stephen Keshi
Mai horas da 'yan wasan Najeriya Stephen Keshi

A karshen makon da ya gabata ne aka buga wasannin share fage na shiga gasar neman kofin nahiyar Afirka a shekara mai zuwa, inda kungiyoyin kwallon kafa daga kasashe daban daban suka fafata.

Talla

Wasu daga cikin wasannin da aka buga kuwa sun hada da kararwar da aka yi tsakanin Algeria da Habasha inda Algeria ta yi nasara ci 2-0, yayin da Kamaru ta yi tattaki har zuwa birnin Lumunbashi domin doke Jamhuriyar Dimokuradiyyar Congo ci 2-0.

Haka zalika daya daga cikin zakaru a nahiyar ta Afirka wato Ghana, a nata wasan ta yi canjaras da kasar Uganda ci 1 kowanne, yayin da Najeriya wadda ke rike da kofin gasar, ta sha kashi a hannun ‘yan wasan Congo Brazaville ci 3-2, kuma a buga wasan ne a garin Calabar da ke kudancin Najeriya.

Kasashen Senegal, Afirka ta Kudu da kuma Guinea Conakry, dukkaninsu sun yi nasara a wasannin da suka buga, inda Senegal ta lallasa Masar ci 2-0, Guinea ta doke Togo ci 2-1, yayin da Sudan ta sha kashi a hannun ‘yan wasan Afrika ta Kudu ci 3-0 a birnin Undurman.

A can kuwa birnin Yamai, kasar Cap Verde ce ta doke Jamhuriyar Nijar ci 3-1 kamar dai yadda ita ma Burkina Faso ta doke kasar Losetho ci 2-0 a karawar da suka yi a birnin Ouagadougou.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.